Home / News / Top Trending News Today / A yayinda Amurka ta katange Najeriya daga siyan jiragen sama na yaki, sojojin sun sami wannan
vllkyt5mdp956used.1fca6396

A yayinda Amurka ta katange Najeriya daga siyan jiragen sama na yaki, sojojin sun sami wannan

– Wasu matasan Arewa ya bukaci sojojin Najeriya da su yi watsi da dukkan yaunkuri wasu yan Najeriya na son rushe masu kokarin sun a yaki da masu tayar da kayar baya

– Kungiyar sun kuma yi kira ga kafofin watsa labaran Najeriya da su daina bari ana amfani dasu gurin karkata hankali a yakin da akeyi da yan ta’adda a Arewa maso gabas

– Sun bukaci jama’an Najeriya da su yi watsi da rahotanni dake kokarin shafawa sojoji bakin fenti

Buratai

Wani kungiyar matasan Arewa, sashin shugabannin matasan Arewa a ranar Lahadi, 13 ga watan Nuwamba, sunyi kira ga sojojin Najeriya da suyi watsi da dukkan rahotannin karya game da hukumarsu a kafofin watsa labarai.

Sun bayyana rahoton a matsayin ayyukan yan adawa, kungiyar tace dole su koyi mayar da hankali akan aiki na raba Najeriya da yan ta’addan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Hukumar kwastam ta koka kan kashe jami’anta

Kungiyar sun kuma yi kira ga kafofin watsa labaran Najeriya da su janye daga barin ana amfani dasu gurin karkatar da hankali daga yakin da akeyi da masu tayar da kayar baya a Arewa maso gabas.

Da yake Magana a taron manema labarai a Kaduna, shugaban kungiyar ta kasa baki daya, Abubakar Abubakar ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da rahotannin dake yunkurin shafa bakin fenti ga sojoji.

Ya ce sadaukarwan da dakarun sojojin Najriya keyi don ceto kasar ya cancanci godiya daga dukannin yan Najeriya.

Abubakar ya kuma bayyana rahotanni da akayi kwanan nan na cewa gwamnatin tarayya ta hayo sojojin haya don su gudanar da yaki da yan ta’addan Boko Haram a matsayin aikin masu fasadi da inganta zargi.

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: