Home / News / Top Trending News Today / An sake gano wasu kudade $175m dangane ga Patience Jonathan
vllkyt4nf2hvmpjdv.c2a03fa2

An sake gano wasu kudade $175m dangane ga Patience Jonathan

– Uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan,ta shiga uku yayinda hukumar EFCC tayi bibitan wasu kudi $175m asusun ta

– Matsalan shine an cire kudin ba tare da sanin wanda ya cire ba

– Wannan sabon kudi ne banda $15.5m da aka daskarar kwanaki a banki

Hukumar EFCC

Jami’an hukumar EFCC

Uwargidan tsohon shugaban kasa , Patience Jonathan,ta shiga uku yayinda hukumar EFCC tayi bibitan wasu kudi $175m asusun ta. Matsala daya shine an gano cewan an cire kudin daga asusun ba tare da sanin wanda ya cire ba.

Game da cewar Jaridar the Nation, an gano kudin a asusun wata kamfani Pluto Property and Investment Limited, daya daga cikin kamfanoni masu alaka da Mrs.Patience Jonathan.

KU KARANTA: Kuma dai: Shugaba Buhari ya kara ganawa da Bukola Saraki

Jami’an EFCC sun samu cewan an bude asusun bankin ne a ranan 30 ga watan Nuwamba 2013 da suna Pluto Property and Investment Limited, mai lamba 2110002238.

Kudaden da aka tura sune: 21/2/2014—$46,500,000; 24/2/2014—$31,000,000; 31/3/2015—$49,250,000; 1/4/ 2015—$49,000,000

“EFCC na binciken yadda aka tura wadannan makudan kudin kimanin shekaru 2 da kafa kamfanin ba tara da cewa sunyi wata kwangilan a zo a gani ba. Muna zargin cewa wannan wata asusu ce da ake boye kudadem gwamnati. An kai kudaden banki ne a hannu , wanda ke tabbatar da cewan kudin sata ne.”

Amma, wani ma’aikacin tsohon shugaba kasa, yace hukumar EFCC na son tilasta shi yayi shaida akan Patience Jonathan bisa ga laifin satan kudin al’umma.

Ku biyo mu a shafin sada ra’ayi da zumuntar mu ta Tuwita: @naijhausacom

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: