Home / News / Top Trending News Today / Daga hawa: Sabon Gwamna ya canza tsari
vllkyt26qgccl4hvbg.d3742f59

Daga hawa: Sabon Gwamna ya canza tsari

– A ranar Asabar aka nada Mista Godwin Obaseki a matsayin sabon gwamna na jihar Edo

– Daga hawan sa, ya canza tsarin tsohon Gwamna Oshiomole na raba abinci

– Sabon gwamna Obaseki yace kowa sai ya dage ya nema abinci

Obaseki (2)

A Ranar Asabar dinnan da ta wuce, aka nada sabon gwamna a jihar Edo. Mista Godwin N Obaseki. Da hawan gwamnan, yace shi zai sha ban-ban da tsohon Gwamna Adams Oshiomole. Gwamna Obaseki yace shi bai yarda da rabawa mutane abinci ba, yace sai dai fa kowa ya je ya nema.

Sabon Gwamna yayi wannan jawabi ne a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Benin. Obaseki yace shi aiki zai yi ba siyasa ba. Yace a baya an buga siyasa ne saboda halin da aka samu Jihar, amma yanzu aiki za ayi tsantsa don kuwa abubuwa sun canza.

KU KARANTA: Jihar Edo; An yi sabon Gwamna

Sabon Gwamna na Jihar, Godwin Obaseki yace ba za a bar kowa a Gwamnatin sa ba, sai dai lokacin raba abincin kummalo dsr ya wuce. Sabon Gwamna yake cewa kowa sai ya tashi ya nemo abin da zai sa a bakin sa.

Obaseki ya zama Sabon Gwamna na Jihar bayan wa’adin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya kare. Gwamna Obaseki ya yabawa Kwamared Adams Oshiomole da irin ayyukan da ya zuba a Jihar a lokacin karbar mulkin, yace Oshiomole namijin gaske ne. Mutane da dama irin su Yakubu Gowon, Alhaji Aliko Dangote, Bukola Saraki suka halarci nadin sa.

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: