Home / News / Top Trending News Today / Na kusa da Shugaba Buhari ba su san aiki ba-Sanatoci
vllkyt7a0jv070i5c.c8636107

Na kusa da Shugaba Buhari ba su san aiki ba-Sanatoci

– Kakakin majalisar dattawa na kasa nan, Abdullahi Sabi yace mashawartan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba su san aikin su ba

Mai magana da bakin Sanatoci na kasar nan yace Fadar Shugaban Kasa ta aiko takarda zuwa Majalisa ba tare da bayani ba

– Sanata Sabi Aliyu yace wannan zai kara jagwalgwala alakar da ke tsakanin Sanatoci da shugaban Kasa

Sanatoci sun ce Mashawartan Shugaba Buhari suna da sakaci

Sanatoci sun koka da yadda ake tafiya a Gwamnatin Shugaba Buhari, Sanatocin Kasar sun ce ba su san inda aka dosa ba a Gwamnatin Buhari wajen gyara tattalin arzikin Kasar. Sanaotoci sun ce har yanzu ba su ga inda Shugaba Buhari ya dosa ba da manufafoin sa.

Wasu daga cikin Sanatocin da suka yi hira da Jaridar Punch, suka ce su ba adawa suke da Shugaba Buhari ba, amma dai maganar gaskiya na kusa da shi ba su san abin da suke yi ba. Sanatocin sun koka da yadda Shugaban Kasar ya aiko da takarda ba tare da wani gamsasshen bayani ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kara zama da Bukola Saraki

Shugaba Buhari yana rokon Majalisar Dattawar Kasar nan su amince da a karbo bashin kudi Miliyan $29.9. Sai dai Sanatocin sun ce ba su yadda ba. Sanatocin sun ce ana bukatar Shugaba Buhari ya aiko da wasu bayanai masu matukar amfani tun watan Jiya, amma har yau bai turo ba.

Kakakin Majalisar Dattawa na Kasar nan, Abdullahi Sabi yace ta tabbata Mashawartan Shugaba Buhari ba su san aikin su ba. Mai magana da bakin Sanatoci na Kasar yace masu taimakawa Shugaba Buhari suna da sakaci kwarai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: