Home / Nigerians Trending News Today / Tsagerun Neja Delta sun yi barna
vllkyt1d1ggi5onp7o.ff92d4ad

Tsagerun Neja Delta sun yi barna

– Tsagerun Neja Delta sun fasa wani babban bututun man fetur na Kasar kwanaki

Tsagerun na Neja-Delta sun fasa Bututun Forcados, hakan ya jawo mai ya kwarara cikin yankuna na Neja Delta kuma Kamfanin Shell na kokarin rage kwararar man

Tsagerun Neja-Delta sun yi barna

Bututun mai

Kwanakin baya wasu Tsagerun Neja-Delta suka fasa wani Babban bututun mai na Forcados da ake fitar da mai wajen Kasar nan domin a sayar. Sai dai fa baya ta zo da kura, don yanzu haka wannan aika-aika ya jawo babbar barna a Yankin nan na Neja-Delta.

Fashewar bututun ya sa mai ya kwarara kwarai a Yankin. Yanzu haka, man fetur ya shiga cikin ruwa da sauran Yankin na Neja-Delta saboda fashewar wannan babban bututu. Jaridar Punch tace wannan bututun ne yake fitar da mai wajen Kasar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai saki Nnmadi Kanu?

Bututun Forcados na Kamfanin Shell ne, yana Garin Burutu da ke Jihar Delta. A Ranar 9 ga Wata kuma Tsagerun na Neja-Delta suka fasa bututun. Wannan abu dai ya saka al’ummar Ogulagha cikin matsala. Man fetur ya kwarara zuwa cikin Garin da kuma cikin ruwa.

Yanzu haka dai Kamfanin Shell ta tura wasu Ma’aikatan ta domin kare kwararuwar man zuwa sauran wurare. Tsagerun Neja-Delta Avengers ne suka yi wannan barna ko can.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: