Home / Nigerians Trending News Today / An karrama Dangote da digirin Dakta a Ibadan
vllkyt5eei5bei12m.66e79c96

An karrama Dangote da digirin Dakta a Ibadan

– Jami’ar Ibadan ta karrama hamshakin attijiri Aliko Dangote tare da wasu manyan mutane biyu a Najeriya da Digirin girmamawa ta Dakta

– Dangote ya ce zai bawa jami’ar wata kulawa ta musamman daga bangarensa, ya kuma bayara da gudunmawar naira milliyan 250 don kamala wani aiki da a ke yi a jami’ar

Dangote 2

Mai alfarama Sarkin Musulmi tare da Dagote a yayin bikin bayar da digirin karramawa

An karrama shugaban na rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da digirin girmamawa na masanin kimiya (D.Sc.) daga jami’ar Ibadan (UI).

An karrama Dangote, tare da wasu manyan mutane biyu, Farfesa Niyi Osundare, da kuma Cif Bode Amao, a wani bikin yaye daliban da suka kammala karatunsu karo na 68 a ranar 17 ga watan Nuwamba, a cewar jaridar Daily Trust.

A jawabinsa a wurin bikin, Dangote ya ce, zai saka jami’ar cikin jerin jami’o’in da za su rika samun kula ta musamman daga gare shi, “na yarda cewa jami’ar ya kamata ta sami kula ta musamman ba wai don kasancewarta tsohuwar jami’a a Najeriya ba, sai dan kasancewar gudun mawar da ta ke bayarwa ga al’ummar wannan kasa, tare da isasshen kudi, na aminta cewa jami’ar za ta iya yin gogaiya da manyan jami’oi na duniya.”

KU KARANTA KUMA: Karanta Labarin Muloniya mai sayar da kaji

Dangote ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya daukar nauyin ilimi ba kacokam, “tsarin hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu, na (PPP) zai taiamaka kwarai, na yarda cewa idan akwai hadin gwiwa tsakanin kamfanoni masu zaman kansu za su iya samar da fiye da kaso biyu cikin dari ta hanyar hada hannu da gwamnatin jiha da ta tarayya wajan samar da kudade ga manyan makarantu.”

Attajirin ya kuma ba da gudunmawar Naira milliyan 250 ga Jami’ar ta Ibadan, yana cewa, “muna fatan wannan zai tamaka wajen kammala ayyukan da jami’ar ta sa a gabanta.”

A biyo shafinmu na Tiwuta: @naijcomhausa

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: