Home / Nigerians Trending News Today / APC ta fara watsewa? Tinubu da wasu gwamnoni sun kauracewa gangamin kamfe
vllkyt4f22uch96t5.ed80cc83

APC ta fara watsewa? Tinubu da wasu gwamnoni sun kauracewa gangamin kamfe

– Jamíyyar All Progressives Congress (APC) ta yi taron yakin neman zaben jihar Ondo a yau Asabar, 19 ga watan Nuwamba

– Shugaba Buhari ne ya jagorance su tare da gwamnonin APC

– Bola Ahmed Tinubu da wasu jigajigan jam’iyyar sun ki halartari taron

– Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na mara ma Rotimi Akeredolu SAN, baya a zaben gwaman jihar Ondo da za’ayi kwanan nan

Tinubu

Babban jigo a jam’iyyar APC mai mulki a kasar nan Ahmed Bola Tinubu tare da wasu gwamnoni daga yankin kudu-maso yammacin kasar nan sun kauracewa taron gangamin. Kamfe da akayi na zaben gwamnan jihar Ondo dake tafi a cikin wani yanayi mai daure kai.

Taron gangamin dai ya samu tagomashi inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarce shi amma sai gashi gwamnonin dake makwabtaka da da jihar ta Ondo irin su Legas, Osun da Ogun sun kauracewa taron.

Ana dai ta rade raden cewa jam’iyyar ta APC a yankin ta shiga wani rudani ne tun bayan da aka yi zaben fitar da gwani inda dan takarar da Ahmed Tinubu ke goyawa baya ya sa kasa.

Ku Karanta: Buhari ya dukufa kan binciken mai a arewacin Najeriya

A wurin taron dai shugaba Buhari ya gabatar da tan takarar na gwamnan jihar karkashin jam’iyyar APC a bainar jama’a sannan kuma ya roki jama’ar jihar da su zabe shi.

A baya dai an ruwaito cewa Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya fara mika-wuya ga matsin-lambar da wasu `yan kasar ke yi cewa ya kamata ya sa baki wajen magance rikice-rikicen da ke damun jam`iyyar su ta APC.

Mutane da dama ciki har da matarsa na korafin cewa ba a damawa da wadanda suka yi wa jam`iyyar dawainiya wajen nadin mukamai.

Kawo yanzu dai shugaban kasar ya gana da gwamnonin jam`iyyar, haka kuma ya fara daukan matakan sasantawa da wasu jiga-jigan jam`iyyar, wadanda ake zargin cewa sun fara juya wa jam`iyyar baya.

Wasu dai sun bada shawara idan za a bada muhakamai na siyasa, a tabbatar an raba tsakanin dukkan bangarori, dan kowa magance korafin cewa ana nuna fifiko.

Ku Karanta: Wani dalibi dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki

Jam’iyyar APC dai na fama da rikicin cikin gida, musamman a rassan jam’iyyar da ke jihohin kasar.

Lamarin da wasu ke ganin cewa matukar ba a shawo kan matsalar ba da dinke barakar da ke tsakanin su akwai jan aiki a gaban jam’iyyar nan gaba.

A baya dai masana sun yi ta kira ga shugaban kasar da ya yi amfani da matsayinsa wajen kashe wutar rikicin jam`iyyar, amma mukarrabansa na cewa ba ya shisshigi.

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

New Music: Harrystone – 'Roll that'

Post Views: 13 This is that kind of song you want to hold on tight …

Leave a Reply

%d bloggers like this: