Home / Nigerians Trending News Today / Yan sanda sun bude wuta kan magoya bayan PDP
vllkyt27dqjlapavl.32c75fe5

Yan sanda sun bude wuta kan magoya bayan PDP

– ‘Yan sanda sun budewa ‘yan jam’iyyar PDP wuta a jihar Rivers a kokarinsuna tarwatsasu daga wani wani ganganmin taro da suka yi a harabar majalisar dokokin jihar na ziyara godiya

– ‘Yan sandan sun kuma kwace na’urar daukar hoto na dan jaridar gidan talbijin a jihar, bayan da ake zargin sun jikkata wani da harbi

Police brutality

An zargin ‘yan sanda da cin zalin magoya bayan PDP a jihar Rivers

An sami hatsaniya a jihar Rivers ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, bayan da ‘yan sandan suka harba barkonon tsohuwa, sun kuma harbi magoya bayan jam’iyar ta PDP wadanda suke kan ziyararsu ta godiya ga majalisar dokin jihar.

PDP 4PDP 3

A wani hoton bidiyo da wani ya dauka da wayar hannu ya nuna yadda wani magoyin bayan jam’iyar PDP ya ke ta burgima a kasa sakamakon harbin bindigar da a ka yi masa, da kuma wani wanda ya ke kwance a gadon asibiti wanda ya ji raunuka a kafafuwansa.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: PDP ta nemi INEC ta daga zaben jihar Ondo

Mun kuma ga yadda ‘yan sandar su ke ta harbawa ‘yan’jam’iyyar barkonon tsohuwa, da kuma harba bindiga a sama.

‘Yan jam’yar sun yi ikirari cewa, a yayin da ‘yansandar suka afka musu, sun kuma kwace abin daukar hoton ‘yan jaridar gidan talabijin din Channels.

Kakakin majalisar jihar ta Rivers Adams ya kalubalanci yadda yan sandan suka afkawa ‘yan jam’iyar ta PDP. Shugaban majalissar ta jihar ta Rivers na nuna rashin jin dadinsa kan faruwar lamarin, ya kuma ce muzgunawar da ‘yan sandan ke yi wa ‘yan jamiyyar ta PDP a jihar ba zai sa su rabu da jam’iyyar ba.

Shafinmu na Tiwuta ne: @naijcomhausa

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: