Home / Nigerians Trending News Today / Yadda yan fashi ke cin karen su ba babbaka a Zamfara (Karanta)
vllkyt24lhkcgpqnng.3ab3b4f4

Yadda yan fashi ke cin karen su ba babbaka a Zamfara (Karanta)

– Rahotanni daga jihar Zamfara arewacin Najeriya sun ce ‘Yan bindiga sun kai kai hare hare a wasu kauyukan kananan hukumomin Maradun da Shinkafi da Maru inda suka kashe mutane da dama tare da sace wasu

– Majiyoyi daga yankin Maradun sun ce kusan mutane 30 aka kashe a harin da ‘Yan bindigar suka kai a kauyen Dan Kamoji a jiya Juma’a

Sannan wasu ‘Yan bindigar da dama sun shiga kauyen Tubali saman Babura a gundumar Birnin Yero cikin karamar hukumar Shinkafi inda suka suka kashe mutane da dama.

A yankin Maru ma rahotanni sun ce maharan sun sace mutane sama da 40 ‘Yan kasuwa da ke hanyar zuwa cin kasuwar Magami tare da kashe ‘Yan sanda biyu a kauyen Ningyado da ke cikin yankin Dansadau.

Ku Karanta: Wani dalibi dan shekara 13 yayiwa malamarsa ciki

Sai dai rundunar ‘Yan sandan Jihar ta ce tana bincike domin tantance adadin mutanen da aka kashe a jerin hare haren.

Kakakin ‘Yan sandan Jihar Muhammad Shehu ya shaidawa majiyar mu cewa har yanzu ba su tantance adadin mutanen da aka kashe ba.

Hare haren na zuwa bayan harin da aka kai wa lebarorin hako zinari a makon jiya a kauyen Bindin cikin karamar hukumar Maru inda aka kashe mutane kusan 40

‘Yan fashi dai sun addabi mutanen kauyukan Zamfara duk da farmakin da rundunar sojin Najeirya ta kaddamar na Operation Harbin Kunama a jihar.

Comments

comments

About Goodness Adaoyiche

Check Also

Craig Ballantyne: I was young, rich, and successful and had crippling anxiety. Here’s how I beat it

Post Views: 24 Tingles ran from the top of my head down to my fingertips. …

Leave a Reply

%d bloggers like this: